Titin Gidan Gwamnatin jihar kano ya zama mafarka ‘Yan sara da suka, tare da masu kwacen wayoyin da dukiyar al’umma kuma hakan na nuna cewa idan gwamnati batai gaggawar magance matsalar ba wannan abu ka’iya hayayyafa, Domin kuwa wadansu bata gari suna fakewa da titin a matsayin babban titi mai tsaro wanda ba kowane zai gane da bata gari ba agun, suna tare mutane suyi musu fashi da makami.

Sau tari al’umma sun sha kokawa a game da wannan titin, kamar yadda wani bawan Allah da aka tareshi a lokacin da yake neman abun Hawa ya tafi gidansa ya bayyana manaβ¦
“Idan mutum ya baro wajejen kofar Gidan Gomnati to fa komai ka’iya faruwa dashi, saboda a iya wajejenne kawai jami’an tsaro suke, Na taho ina tafiya ina neman baburin Adaidata sahu kwatsam sai ga wadansu matasa akalla sunkai su 6, da yake ankirani a wayata zan dauka, sukace inbasu wayar na kalli hannuwansu naga dukkansu da wukake na mika musu daya daga cikin su yace su lalube aljihunana suka lalabe kuma komai na ciki saida suka sacemin”
Mutane da dama sunsha kawo kukansu akan an taresu a wannan titin musamman daga karfe 7:30 zuwa 11:30 na dare a wannan titin.
Shin Meyasa Hakan ke faruwa?
Ta yaya za’a magance wannan matsalar?
Daga: π Rabiu Tijjani Abubakar
Madogara: Kano Online News
