
Bayan kammala aikin bautawa jihar Kano tsayin shekaru 35 – wasu ma duk sun mutu da bakin ciki, zuwa yanzu dai gwamnatin Kano ta gaza biyan ‘yan fansho hakkokinsu tun shekarar 2016
Abin mamaki kuma, sai gashi majalisar dokokin jihar Kano ta sahalewa Maigirma Gwamna Ganduje kudade har miliyan 500 domin ayi wa gadar kofar ruwa ado, bayan an kammala gadar lafiya kalau, amma an sake ware wadannan madudan kudade domin kawata ta.

Shugabannin hukumar fansho ta jiha tace, tana bin gwamnatin Kano bashin hakkokin ‘yan fansho na garatuti fiye da Naira Miliyan Dubu Ashirin da Takwas (#28bn)
Masu iya magana dai sunce komai girman gona tana da kunyar karshe!
