Tattaunawa ta masamman da BIRNIN ZUCIYA

Group din WhatsApp mai suna BIRNIN ZUCIYA karkashin jagorancin Dr Abba Nura yayi tunani wajen hada kuɗi domin ciyarwa ga masu bukata a cikin Ramadan a wannan shekara.

Kamar yadda muka zanta da wanda ya kirkiri group din na BIRNIN ZUCIYA Alh. Ibrahim Ali Ahmad wanda akafi sani da (Mu’azzam) ya sanar da kafar sadarwa ta Qalubale yadda aka kafa wannan group kuma menene dalilin kafashi da kuma manufofinsa?

As-salamu alaykum warahamatullah wabarakatuh, da farko muna godiya ga Allah daya bamu dama domin gabatar da wannan tattaunawa a wannan rana ta Lahadi 7 ga watan Afrilu 2024 wacce tazo daidai da 28 ga watan Ramadan 1445 AH

Kai tsaye, kamar yadda mai gabatarwa ya tambaya, zan bayyanawa duniya cewa wannan group na WhatsApp mai suna BIRNIN ZUCIYA an kirkireshi ranar Alhamis 28/5/2020 bisa dalilai kamr haka;

❤️ *BIRNIN ZUCIYA GROUP*
*MANUFOFIN WANNAN GIDA*
An bude wannan gida ne mai suna *BIRNIN ZUCIYA* domin sada zumunci, fadakarwa, ilimantarwa, taimakon juna da kuma kawo abubuwa da suka shafi al’amura na yau da kullum – bisa mutumtaka da girmamawa, duk tsokana da muke yi wa junanmu, mu dauka raha ne, ba gaskiya ba ne – laifi ne cin fuska ko cin zarafi a wannan gida.
❤️ NISHADANTARWA
* FADAKARWA
* ILIMANTARWA
* RAHA/ZOLAYA
* SADA ZUMUNCI
* TAIMAKON JUNA
*SHIRYE-SHIRYEN DA MUKE GABATARWA*
(Programs)
*1. KIWON LAFIYA*
*2. RAYUWA A MUSULUNCI*
*3. TAURARON MAKO*
*4. FADAKARWA GA MA’AURATA*
*5. INA MUKA DOSA*
*Wasu shirye-shiryen nanan tafe nangaba insha Allahu, Allah yabamu nasara Ameen*
✍️ DOKOKIN WANNAN GROUP
1. ✅ Ba’a sanya videos, hotuna ko furuci na batsa.
2. ✅ Mu kiyaye mutuncin junan mu, ta hanyar girmama junanmu da daraja kalamai.
3. ✅ Dokane cin zarafin wani ko zaginsa ko yin fada, in wani yayimaka ka sanarwa shuwagabannin gidan zasudauki mataki.
4. ✅ Kada ka tursasa wani ya amince da tunanin ka ko ra’ayin ka.
5. ✅ Dokarmu tahana dauko zancen wani gida zuwa wannan gida ko zancen gidan mu zuwa wani gida.
6. ✅ Wajibi ne mambobi su dinga amsa sallama, sannan su dinga yin magana a group akai-akai, musanman insuna Online ko in ana gabatarda shiri suyi liking.
7. ✅ Munhana tallace-tallace ko tallen kaya kona group a cikin wannan gida.
8. ✅ Mun haramta tattauna maganar siyasa, Jam’iyya, ko batun akidar addini, ko kwallo, ko yin posting game dasu.
9. ✅ Laifi ne kawo saɓani daya hada ku a wajen group zuwa cikin wannan group.
10. ✅ Dolene mu kasance masu kiyaye wadannan dokoki tareda mutunta shugabancin wannan gida, zaka iya kawo shawarar duk wani abinda zai kawo cigaban wannan gida ko mutanan cikinsa.
11. ✅ Za’a iya yin gyara a wadannan dokoki a duk lokacin da bukatar haka ta taso.
Muna maraba da dukkan gudumuwar mambobin wannan gida ta kowanne bangare.
Allah yabamu nasara yakara hada kawunanmu Ameen.
✍️ Shuwagabannin wannan gida su ka rubuta.

Kamar yadda Alh Ibrahim Ali Ahmad (Mu’azzam) yayi cikakken bayani tun daga ranar da aka kafa wannan group, haka kuma yayi bayani na dalilai na kafawa da kuma manufofin kafawar, har ma da abubuwan da group din ke gabatarwa domin amfanuwar jama’a.

Zamu so jin yadda ciyarwar Ramadan ta gudana inda Mu’azzam ya sake yin bayani kamr haka;

Mun samar da kudi ne ta hanyar yin karo-karo da group din BIRNIN ZUCIYA ya nemi shugabanni da mambobi su bayar domin a gudanar da wannan aikin alkhairi da sunan wannan group, ba tare da bata lokaci ba, dayawa suka karbi kiran kuma suka bayar da abinda zasu iya bayarwa

Gombe

Kamar yadda muka ga hotuna da videos, group din BIRNIN ZUCIYA yayi namijin kokari wajen samar da abin buda baki ga masu azumi a wasu jihohi guda biyu Yobe da Gombe.

Yobe

Alh Mu’azzam wane dalili yasa aka gabatar da wannan ciyarwa a jihohi daban daban?

Dalilin mai sauki ne, duk wani group na social media Yana kunsar mutane daga jihohi daban-daban, wani lokaci ma zakaga har da mutane daga makwabtan kasashe kamar su Chad, Niger, Libya da dai sauransu.

Wannan dalili yasa muka dauki jihohi biyu domin mu fara dasu, kasancewar akwai mambobin mu a jihohi sai muka tuntubesu su ka amince muka basu amanar yin wannan aiki da sunan group din BIRNIN ZUCIYA, mun tura masu kudaden da aka tara kuma sun aiwatar da abinda ya dace, sannan shugabancin group da mambobi sunji dadin yadda aka tsara kuma aka gudanar da abin cikin sauki.

Gombe
Yobe

Alh. Mu’azzam, zuwa yanzu mambobin group sunkai nawa?

Zamu so jin su waye shuwagabanni a group din BIRNIN ZUCIYA

A halin yanzu shugabanni 14 muke da su, sai kuma idan an hada su da MAMBOBI anyi jimla, gaba daya mu dari da goma sha daya (111) gasu kamar haka;

Chairman – Dr Nura Abba
Vice Chairman – Hajiya Fattu Khalid Usman
Secretary – Alh. Rabi’u (My Fans)
Deputy secretary – Muhammad Bukar
PRO l – Omar Farouk Sani Fagge
PRO ll – Malam Ibrahim Khalil (Sardauna)
Woman Leader – Hajiya Fatima (Hajiyan Kabo)
Deputy Woman Leader – Hajiya Fatima (Maman Islam)
Welfare Officer l – Hajiya Zainab (Anty Zee)
Welfare Officer ll – Musa Sani
Financial Secretary – Manu Ali Bima
Treasurer – Ibrahim Ali Ahmad (MU’AZZAM)
Auditor – Baba Balarabe
Chief Whip – Alh Rabi’u (Dee Rabs)

Akwai kwamatin amintattu masu ruwa da tsaki a cikin wannan tafiya, wadanda muke kira Board of Trustees (BoT)

Wannan kwamati nine nake jagorantarsu a matsayina na Chairman sai kuma mataimakina Haruna Ibrahim

Yanzu haka wannan gida ya tafi shekara 4 da kafawa, gashi kai ɗaya nasamu a office domin amsa tambayoyin mu, shin a tsayin wannan lokaci wace nasara wannan group na BIRNIN ZUCIYA ya samu kuma wane abu yafi baka jin dadi bisa samar da wannan gida zuwa yanzu?

Gaskiya mun sami nasarori masu tarin yawa duba da yadda muka shafe shekaru hudu cikin mutumtaka da girmamawa batare da samun tashin hankali ba.

Abu na biyu shine yadda muke gabatar da shirye-shiryen da suke amfanar da jama’ar gidan

Abu na uku shine yadda muka kulla zumunci tun muna ganin juna a hoto, har yakai muna iya zuwa garuruwa ko unguwannin junanmu domin sada zumunci

Sai kuma wannan ciyarwa da mukayi a wannan wata na Ramadan, shine babban abinda yafi bani dadi a duk tsayin wadannan shekarun

Alh. Mu’azzam jagoran wannan tafiya ta BIRNIN ZUCIYA, bamu sani ba, ko akwai wani danasani da kayi bayan ka kirkiri wannan tafiya?

Har ka bani dariya, maganar gaskiya tun bayan kirkirar wannan gida zuwa yanzu shekara hudu, babu wani danasani, sai jin dadi da farin ciki

Amma akwai abubuwan da bazan manta dasu ba, na farko dai mun hadu da mutane, inda duk ka tara mutane dole akwai zaman hakuri, sakamakon mabanbantan tunani da za’a samu, a halin yanzu akwai mutane da muka zauna dasu a wannan gida kuma basanan tare damua wannan gida, sakamakon haka har yanzu muna tare dasu a gefe guda muna sada zumunci.

Wasu mata ne, sunyi aure, kuma sun bada gudunmawa matuka wajen cigaban gidan da dorewarsa, muna yi masu fatan alkhairi, Allah ya zaunar dasu lafiya a gidajen aurensu.

Daga karshe, wace shawara zaka ba shugabanni da mambobi har da ma sauran masu ire-iren waɗannan gidaje a kafar sadarwa ta zamani?

Alhamdulillah shawarwarin da zan baiwa shugabanni da mambobi sune;

Na farko duk abinda za’ayi a irin waɗannan gidaje a dora shi bisa doron niyyar yin abin domin Allah, sannan a nufi Allah yayi jagora, sai kuma taimako ga dukkanin ma’abota gidan, ta hanyar ilimantarwa, fadakarwa da duk wani abu da zai kawo cigabansu

Na biyu, a dinga mutunta juna, a girmama juna, a tausasa kalamai ga juna

Na uku, a dinga yin hakuri da juna idan wani yayi wani abu wanda ya sabawa dokokin gidan a fahimtar dashi kuskuren daya aikata a cikin masalaha

Na hudu, duk wata rashin fahimta data shafi tsakanin ƴaƴan group su kwantar da hankalinsu kuma su sanar da shugabanni, su kuma shugabanni suyi gaggawar daukar matakin warware matsalar cikin ruwan sanyi

Allah ya bamu dacewa, ya karo mana cigaba da walwala a rayuwarmu, Allah ya zaunar damu lafiya, ya zaunar da kasarmu lafiya, Allah ya kyautata zuriyarmu, ciyarwa da wannan gida yayi a wannan wata mai albarka na Ramadan Allah yasa a mizani, ya hada mu cikin ladan gaba daya.

Alh. Mu’azzam muna godiya da wannan lokaci da ka bamu, sai wani lokaci idan bukatar haka ta taso.

Published by Ibrahim Ali Ahmed

Political Analyst

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Design a site like this with WordPress.com
Get started