Ana gumurzu tsakanin ‘yan sanda da ‘yan kungiyar Shi’a

Awa daya data gabata an fafata tsakanin mabiya darikar Shi’a da jami’an ‘yan sanda a birnin Tarayya Abuja Najeriya.

‘Yan Shi’a sun fito zanga-zanga domin neman gwamnati ta saki jagoransu Zakzaky inda sukayi arangama da jami’an ‘yan sanda India akayi dauki-ba-dadi a tsakabinsu kamar yadda giean radio na BBC ya bayyana.

#Qalubale

Idan kaji tana yawan furta maka kalamai kamar haka

Daga Sani Adamu Hotoro:

(1) #Nifa_Idan_Ka_Auren_baka_Isa_Kayi_Min_Kishiya_Ba

(2) #Baka_Isa_Ka_Rabani_Da_KawayeNa_ba

(3) #Baka_Isa_Ka_Hanani_Chatting_Ba

(4) #Dole_Ne_Duk_Lokacin_Da_Unguwa_Ta_Kama_Naje

(5) #Sannan_Nice_Zan_Ke_Fita_cefane_Da_zuwa_Kasuwa_Siyayya

To tabbas idan kaji wannan kalamai a bakin yarinya ka hakura da ita duk son da kake mata indai ba ajali ne yake janka ba
kuma wllh ko ba ajali zata gurbata maka tarbiyyar yaran da zaku haifa

Allah mun gode maka da ka bamu mata na gari

GA A INDA MATSALAR TA SAMO ASALI

Daga Adam M Panda:

A dan kwarya-kwaryan binkicen da na gabatar mun gano wasu daga cikin musabbabin da suke sauya dabi’un matanmu daga abokan rayuwa zuwa abokan fargaba

Matsalolin sune
Kawaye
Wayoyi
Litattafai
Kalle-kalle

1. KAWAYE
Hakika yin mu’amala da matanmu da ‘ya’yanmu keyi da gurbatattun Kawaye yana matukar tasiri wajen lalata tarbiyyar da muke dora matanmu da ‘ya’yanmu akai, don haka ya zama. wajibi garemu mu tantance su waye kawaye iyalanmu a gidajenmu da kuma makarantun ‘ya’yanmu

2. WAYOYI
Ba makawa wayoyin da iyalanmu kanyi amfani da su na da matukar tasirin wajen kyatata tarbiyyar iyalanmu ko gurbata ta.

3. LITATTAFAI
A wannan yanayi da muke ciki karance-karancen ko sauraron masu karanta Litattafan soyayya wani bangare ne na wasu daga cikin iyalanmu, wanda wani lokacin ma zaka iya cewa kaso ne mai yawa a lokutansu, harma wasunsu suna fifita wadancan karance-karance fiye da hakkokin da suka rataya akansu na mazajensu ko iyayensu, da dama wasu mutanen sun sha yin korafin cewa “Iyalensu sun sha yi musu asarar dukiya sakamakon shagaltuwa da irin wannan karance-karance”

4. KALLON FINA-FINAI
Tabbas wannan dabi’a ma tana matukar gurbata tunanin iyalanmu, wanda za kaga Uba ko Mai gida ya sayawa iyalansa kayan Kallo amma babu ruwansa da sanin irin tashoshin ko kasansunan da suke kallo wanda lokuta da dama, Makiya Allah nayi amfani da wannan dama wajen haska gurbatattun fina-finan da zasu iya gurbata tunanin iyalanmu.

A karshe da wannan da binkice nakeso nayi amfani wajen tuna mana Hadisin Shugaba S.A.W wanda yake mana
“KULLUKUM RA’IY WA KULLUKUM MAS’UULUN AN RA’IYYATIHI”

MA’ANA
Dukkanku Makiyayane kuma kowa abin tambayane akan kiwon da aka bashi

(Sadaqarrasulul-kareem)

ABIN KUNYAR DA KE ADDABAR AKASARIN HAUSAWAN AREWA

Daga Sayyada Muhammad Jidda

Sai ka je gun taro ka ji an kamo sunan wani ƙasurgumin tsohon ma’aikacin gwamnati ko ɗan Siyasa, ana karantowa tarihin rayuwarsa da irin gwagwarmayar da ya yi a fagen aiki da mabambantan muƙaman da ya taɓa rikewa a rayuwarsa.

Ka ji an ce tsohon kaza tsohon kaza tsohon kaza da kaza, tun daga matakin ƙasa, sai an kai ga ambato irin muƙami ko matsayi na ƙololuwa da ya taɓa rikewa a rayuwarsa, amma fa idan ka bincika da ƙyar da jiɓin goshi ka iya samun aƙalla mutum goma ko ƙasa da haka da ya iya taimakawa su ka samu aikin gwamnati ko jarin kasuwa ko tallafin yin karatu ko ƙaro karatun.

In ko ka yi sa’a ka samu ƴan mutanen da ya taɓa taimakawa sai ka ga ƙila duk daga ƴan uwansa sai dangin matarsa. Wai hakan ma shi ne me ɗan imani da ƙaunar al’ummar.

Kuma fa ƙila gogan a lokacin da ake karantowa tarihin rayuwar tasa fankama ya ke ya na yake haƙora ya na baza babbar riga wai shi nan daɗi ya ke ji ana kambama shi a cikin taron al’umma.

Kuma wani ƙarin abin haushi, su ma taron al’ummar dan rashin sanin kai, ƙila a lokacin da ake kambama shin yaƙe haƙwara su ke su na yi masa tafi raf! Raf! Raf!!! Wai ga mutum mai daraja. Kaico!

Mutum ba zai fahimci kuskurensa ba, sai ya gama riƙe muƙaman ya saki ko sun sake shi, kuma ba fata ake ba in Allah ya jarabce shi da wata jartabawa ta rayuwa sai ya rasa masu taimaka masa. Saboda shi ma babu wanda ya taimakawa.

Ba ma wannan ba, aje ma babu jarrabawar, ko irin ƴar ziyarar nan da gaisuwar nan jifa jifa da mutanen da aka taimaka su ke zuwa yi wa wanda ya taimake su bayan ya gama aiki ya dawo gida, sai ya rasa masu zuwa masa. Saboda bai yi wa kowa komai ba.

Wallahi yadda mu ke da mutane masu manya da matsakaita da ƙananan muƙamai cikin aikin gwamnati da Siyasa da kasuwanci a ciki da wajen ƙasar nan da ace za mu yi tsari me kau na tallafawa al’ummarmu, ba shakka za a samu cigaba da sauƙin rayuwa fiye da yadda ake tsammani.

Amma ɗabi’ar nan ta kƴashi da hassada da muguntar kai-da-kai ita ta ke cigaba da daƙile cigaban al’ummar Hausawa.

Allah ya kyauta ya kuma ganar da mu, ya ba mu ikon gyarawa.

Tina Baya…..

A rana irin wannan shekaru biyar da suka wuce a birnin Kano ina nufin 9/6/2014 jama’a sunyi zanga -zanga harma da kone-kone domin nuna kyamar nadin Sarki Sunusi Lamido Sunusi II da Gwamnan wancan Lokaci wato Rabi’u Musa Kwankwaso yayi sabanin wanda ya kamata a nada.

Ko shakka babu a wancan lokaci Kwankwaso yayi wa mutane karfa-karfa ya tilasta musu son zuciyarsa, sai gashi tarihi yana neman maimaita kansa, inda Gwamna Ganduje ya raba masarautar gidan biua (5) haka kuma yake tuhumar badakalar kudi da majalisar masarautar tayi wanda zai iya yin tasiri wajen yin awan gaba da rawanin Sarkin.

Gwamna Ganduje yana kokarin saisaita gidan sarautar na Kano domin yayi daidai da bukatun jama’a sai kuma wasu mabiyan siyasar Kwankwaso da masu mu’amala dashi ta harkar jarida da lauyoyi harma da shi kansa Kwankwason ke tunanin wai Gwamna Ganduje nayiwa mutane karfa-karfa inda suke tuhumar manyan Kano da masu fada aji sunyi shiru sun zubawa Gwamnan ido yanayin abinda yakeso.

Wasu ‘yan jarida da lauyoyi suna alakanta rashin zama lafiya a Kano duk da cewa mudai muna zaune lafiya cikin kwanciyar hankali.

Akwai wasu marubuta da sukayi rubutu a irin wannan rana kamar haka;

1) Prince Dan Sardauna

Jun 9, 2014 at 23:07

Ga abin da wani ya turo mana yace:
Billahillazi lailaha illahuwa narantse da alkur ani idan nayi karya kada allah yakaini gobe kuma kada allah yabani abinda nake nema duniya da lahira nakara rantsewa da alkur ani amatsayina na musulmi dan majen kano wanda akace shine sarkin kano ayanzu kudi yabayar yasayi sarautar kano kuma wanda yayi financial kudin shine wannan fitaccen dan kasuwar wato dahiru mangal wadanda akbawa kudin sune kamar haka. Makama. Miliyan dari. Sarkin dawaki maituta. Miliyan dari. Sarkin bai. Miliyan dari. Madaki. Milyan. dari. Sai babar giwar wato governor kwankwaso wanda yasamu rabo mafi tsoka har naira biliyan biyu. Yasubhanallah allah dangirman zatinka kanunamana karshen wadannan azzalumai allah munbarka dasu.

2) Jameel Sabo

Jun 9, 2014 at 01:01

INNA MAMAKIN MASU CEWA SUNAIWA MAIGIRMA GWAMNA TA’AZIYYAR MUTUWAR MAI MARTABA SARKI,
INDAI YA KAMATA AYIWA GWAMNA TA’AZIYYAH TO LALLAI YA KAMATA AYIWA ABUBAKAR SHIKAU TA’AZIYYAR MUTANEN DA HARE HAREN BAMA BAMAI YA HALLAKA

3) Na’Allah Raheemeeb

Jun 9, 2014 at 06:37

It seems so very easy for Governor Kwankwaso to reverse every decision made by a dignitary at will within his jurisdictions, provided that it doesn’t go well with his liking, yet, Governor Kwankwaso feels free to mention his unchallenged, even though it doesn’t go well with humanity, thinking that he holds the ace. Yes, he holds the ace but he doesn’t hold the crowned ace!

When will the ace he holds got to be crowned? The only question to baffles his brain is the populace who were all out to shame holdouts like Kwankwaso to reverse his decision too.

Now, who holds the JOKER?

Duka wadannan marubuta sun nuna kyamar abinda Kwankwaso ya yi na tozarta masarautar Kano a wancan lokaci, don haka Qalubale gareku masu aibata Gwamna Ganduje da masu jawowa Kano fatan tashin hankali daga kan ‘Yan jarida, lauyoyi, magoya bayan siyasar Kwankwaso da mabiya Sarki Sunusi II, ku shiga runbun ajiyarku ku zakulo mana abinda kukayi wanda zai nuna kishin Kano a wancan lokaci.

EFCC Ta Gurfanar da Jami’an Gwamnatin Kano

Hukumar yaki da cin hanci da karbar rashawa a Najeriya EFCC ta gurfanar da wasu jami’an gwamnati dake kula da hanyoyi da cunkoson ababan hawa na Jihar Kano a gaban wata babbar kotu a Kano.

Wannan ya biyo bayan sojan gona da kuma zamba ta hanyar buga takardun daukar aiki na jabu ga Sabi’u Muhammad, Anas Ahmad da Umar Habibu da sunan daukar su aiki a hukumar Karota da SUBEB daki-daki.

Mutanen da aka gabatar gaban mai shari’a Faruk Lawal sun hada da Abduljalal Salisu da wasu mutane hudu, tuni mai shari’a Faruk Lawal yabaka belin su bisa wasu tsauraran matakai kuma ya dage shari’ar zuwa 27 ga watan 6, 2019.

Labari mai dadi

Labari mai dadi ga duk mai kishin zaman lafiyar Najeriya.

Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya sun yi nasarar ka ma ‘yan ta’addan da suka addabi al’umma a hanyar Kaduna zuwa Abuja sama da mutum 92

‘Yan sandan sun baje su tare da muggan makamai da aka amsa daga hannun su, ciki harda na’urar da suke amfani da ita wajen harbe babbar mota.

Allah ka cigaba da bawa jami’an tsaron Najeriya nasara wajen yaki da ta’addanci a dukkan sassan Najeriya.

SABABBIN MASARAUTUN KANO

Mai Girma Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya rattaba hannu akan sabuwar dokar kafa sababbin Masarautu guda hudu (4) da suka hada da Rano, Karaye, Gaya da Bichi. Da saka hannu a wannan sabuwar doka, gwamnatin Jihar Kano zata nada sababbin sarakuna na wannan masarautun huda da kuma zana iya fadin kasar su, sannan kuma shi Sarkin Kano na yanzu Mallam Muhammadu Sanusi II zai zama Sabon Sarkin Birnin Kano da Kewaye.

Sarkin Birni da Kewaye na da kananen hukumomi guda 10 a karkashin sa da suka hada da

1- Kano Municipal
2- Fagge
3- Nasarawa
4- Gwale
5- Tarauni
6- Dala
7- Minjinir
8- Ungogo
9- Kumbotso
10- Dawakin Kudu

Sarkin Rano kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka;

1- Rano
2- Bunkure
3- Takai
4- Kibiya
5- Sumaila
6- Doguwa
7- Kiru
8- Bebeji
9- Kura
10- Tudun Wada

Sarkin Gaya kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka;

1.Gaya
2.Ajingi
3.Albasu
4.Wudil
5.Garko
6.Warawa
7.Gezawa
8.Gabasawa

Sarkin Bichi kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka;

1- Bichi
2- Bagwai
3- Shanono
4- Tsanyawa
5- Kunci
6- Makoda
7- Danbatta
8- Dawakin Tofa
9- Tofa

Sarkin Karaye kuma zai kasance yana da kananen hukumomi kamar haka;

1- Karaye
2- Rogo
3- Gwarzo
4- Madobi
5- Kano
6- Rimin Gado
7- Garun Mallam

Sarkin Birnin Kano da Kewaye Mallam Muhammadu Sanusi II shine zai zamu Shugaban majalisar zartarwa na Masarautun guda biyar, sannan kuma Sarkin Rano shi zai zama mataimakin sa. Sannan shugabancin wannan majalisar zai zamu na karba karba ne wato rotational inda kowanne shugaba zai shekara biyu inda bayan kammalawar waainda sa kuma gwamnatin jiha na da hurumin kara masa wani waadin karo na biyu.

Sannan sauran yan majalisar masarautar sun hada da

1- Sakataren Gwamnatin Jiha
2- Kwamishinan Kananen Hukumomi
3- Ciyamomin Mulki na kananen hukumomin
4- Hakimai masu nada Sarki bibiyu saga kowacce Masarauta.
5- Wakilcin mutum 5 da Gwamna zai nada.

Saka karshe kuma sabuwar dokar bats hana wani Wanda ya gaji Sarautar Kano daga sauran sababbin masarautun guda hudu ba, zama Sarkin Birnin Kano da Kewaye indai har sun gada.

Salihu Tanko Yakasai
Special Adviser Media
Government House Kano
May 8, 2019.

Meyasa Ake Dora Babba Akan Karami?

NIJERIYA KASAR MAHUKUNTA

A duk lokacin dakaga Hukumomi a Nijeriya sun bawa abu Muhimmanci zakaga sune wadanda zasufi cin moriyar wannan lamarin, kai kace tattalin arzikin Nijeriya an samarda shi ne don masu madafun iko.

Jiya nake jin Majalisar dokokin Kano ta shigar da Kudurin samarwa Speaker da Mataimakin sa tabbataccen Fansho na Mutu ka raba.

Magana ta gaskiya akwai rashin dacewa cikin wannan yunkuri, kowa yasan duk wani Dan Majalisa zama yake tamkar Attajiri idan yana kan mulki da bayan saukar sa, musamman idan yayi hawa sama da daya.

Da ace Talakawa suna da Muhimmanci a wurin ‘Yan Majalisu da dokar dawowa da Ma’aikata kudin Gero da na Rago zamuji ‘Yan Majalisar nan sun dawo da ita, Musamman ma dayake yanzu Muna cikin Ramadhan.

Sau tari zaka samu Ma’aikacin dayayi shekaru 35 na aiki yayi ritaya amma bai Mallaki gidan kansa ba, shin akwai Dan Majalisar dayake kammala zangon farko 4yrs batare da ya Mallaki gida ba balle kuma wanda yakai matsayin Speaker?

Yakamata Mahukuntan mu su farka daga irin wannan Maye na son zuciya dake bugar dasu.

Arzikin Nijeriya na kowa da kowa ne, yadda Mahukunta ke takaice shi a kansu kansu zalunci ne.

Daga Umar Faruq Muhammad

DATTIJON SARKI

Tarihin Masarautar Kano bazai taba Mancewa da Dabi’ar Marigayi Dr. Ado Bayero wajen halin Dattako da daukar Kanawa a matsayin ‘Ya’yan sa dasuka cancanci bayyanannen matsayi iri daya ba.

Saboda yakana da sanin Yakamata in siyasa tazo San Kano Dan Abdu yakan daidaita harshen sa tsakanin mabukatan Madafu a Jihar Kano.

Idan ranar zabe tazo Takawa yakan fita tashar zabe ne badon zabar daya daga mabukatan ba, yana fita ne don zaburar da talakawa wajen fita zaben.

Labari ya tabbata cewa yadda aka yankawa Sarki takardar Zabe (Ballot Paper) haka yake zurata batare da ya dangwalawa ko wacce Party ba.

Sarkin yanayin haka don nunawa ‘Yan takara su duka ‘Ya’ya ne, duk da zuciyar sa tanada wanda take so amma haka yake tankwarata ya daidaita Kanawan sa.

Allah Ya jaddada gafara da Rahma ga Takawa.

MUSULMIN KARSHEN ZAMANI

Duk lokacin da Mallamai ke bayani game da wani tanadi na Rahma da Allah yayi wa Muhsinai cikin bayin sa zakaji Mutane suna nuna zumudin kaiwa ga Wannan Rahmar.

Abin takaicin shine sam bamu da karsashin aikata ayyukan dake Jagorancin kaiwa ga Rahmar.

Daga shekaranjiya duk wanda yashiga Kasuwannin Kano siyan kayan Masarufi don tanadin Azumi zai tarar da canjin Farashi ta hanyar karuwa fiye da satin da yagabata.

Abin tambayar shine ta wacce hanya farashin ke karuwa a duk watan Ramadhan? Shin ba watan Ramadhan bane watan da Rahmar Allah ke samuwa?

Meyasa Yan Kasuwa Musulmi suke tsawwalawa Yan uwan su a wannan watan? Shin a haka muke tunanin Allah zai bamu tasa Rahmar?

Yanzu don Allah bamajin Kunya in Ramadhan ya wuce sai kuma mu sauke farashi?

Gaskiya Musulmin mu na wannan zamanin muna da Matsaloli, da kanmu muke kuntatawa junan mu.

Daga Umar Faruq Muhammad

MAGANAR TSARO A NAJERIYA

YAU da safe Premium Times ta wallafa labarin ‘yan Boko Haram sun kashe sojan Najeriya har 15, tun jiya jaridar The Punch suka bada bayanin ‘yan BH sun karbe wani sansanin soja a Magumeri kusa da Maiduguri tsawon awa hudu. Sun kwashe duk makamai a sansanin, sun yashe sauran kayan yaki.

Da safiyar nan BBC suka rawaito labarin yadda yan fashin daji suka yi wa mutanen Dan gurgu na kasar dagacin DanSadau su 30 kisan gilla.

Kafin wannan Daily Trust ta yi rahoto cewa miyagu akan babura sun je Safana da Batsari a jihar Katsina sun kashe mutane har yanzu ana lissafin adadi. A tsakanin wannan lokaci aka sace Magajin Garin Daura a Dauran a kofar gidansa, akan hanyar Abuja kuma aka sace shugaban hukumar UBEC na kasa da ‘yarsa aka kashe direbansa. Har gida aka je aka kashe mai gadin Bafarawa, aka gudu da wata karamar yarinya.

Kowa ya sani da Filato da Binuwai da Taraba kai da ko ina a arewa ba lafiya.

A wata kidddiga da jaridar THE Punch ta yi, wacce ta samu daga ‘yan sanda ga link din https://punchng.com/1071-killed-685-kidnapped-in-first-quarter-of-2019-ig/amp/, sun ce a cikin wata uku daga Janairu zuwa Maris 2019 kacal, an kashe mutum dubu da 71, an sace 685 a Najeriya, abin yafi muni a arewa, a arewan kuma jihohin Zamfara da Kaduna da Katsina da Sakkwato da Kebbi da Jigawa da Kano.

Sam-sam ban gamsu da matakan da gwamnatin jam’iyyarmu ta APC ta Muhammadu Buhari take dauka ba. Ra’ayin da Rabiu #Biyora yake cewa wai mutanen arewa su hada kansu a yaki wannan abin ban gamsu ba. Wa ye yake da soja da ‘yan sanda da bindiga da kudi da kasar da kasashen waje? Ku ce min Buhari kawai, to ku sani aikinsa ne. Shi ya nada kowa, in wani ya gaza shi zai sallame shi. Don me za a kyale kowa sai cin karensa yake ba babbaka? Shugaba Muhammadu Buhari fa dole ya farka, kuma dole ya katse komai ya dawo ya sauya fasali.
A kasar Srilanka fa da ‘yan ta’adda suka kashe mutum 400, tuni aka kori sufeto janar na yan sanda da ministan tsaro, shi kansa shugaban kasa kujerarsa rawa take yi, komai na iya faruwa.

A nan ma Africa kasar Mali, gaba dayan gwamnatin sauka ta yi saboda an kashe mutum 160 kuma an gaza shawo kan lamarin.

Haka kuma ban amince da ra’ayin Ibraheem A. Waziri ba, cewa system din ne matsalar. Ina son tabbatar muku, matsalar ta mutanen ce, shugaba Buhari ya gwada cire su, ya kori wasu, ya zakulo masu nagarta ya basu dama, ya ga aiki da cikawa. In ba zai iya ba, shima ba lallai ba tilas.

TSARON NAJERIYA SHI NE FIRST

Daga Bello Muhammad Sharada

Direban Babur Mai Kafa Uku Ya Kashe Wani Abokin Aikinsa

Ranar Jummah 3/5/2019 a gadar sama ta kabuba a birnin Kano wani direban babur mai kafa uku ya bugawa wani abokin aikinsa direban babur mai kafa uku almakashi wanda yayi sanadiyyar mutuwar sa.

Kamar yadda kakakin yan sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya bayyana cewa, Abu Hussain mai shekaru 19 ya bugawa abokin aikinsa Mansur Ibrahim mai shekaru 25 almakashi da misalin karfe 2 na rana.

Nan take aka gagguta kaishi asibiti inda rai yayi halinsa, DSP Haruna yace, tuni sun fara bincike inda za’a kika mai laifin Abu Hussain gaban alkali.

Bambamcin Adireshin Masu Kudi Da Namu Talakawa.

Adireshin masu kudi=
House no.3 Road 5c fruity G.R.A opposite lugard cresent.

Adireshin mu talakawa=
Layin kutare gidan mamman mai goro in ka tsallaka kwata na biyu gidan na kallon wata Bola

Wace Godiya Kakewa Allah Bisa Rayuwar Da Ka Sami Kanka Ciki?

Inna lillahi wa Inna ilaihir raji wuun
Allah kakyautata rayuwarmu kasa
Mugama da duniya lafiya

Dan uwa kadubi yanayin rayuwar wadannan bayin Allah basusan fariba basusan bakiba, basusan menene addiniba ballantana ibada,

Allah yabasu saukin rayuwa mukuma yakaremu daga fadawa irin wannan larurar.

Ayi Hankali Da Gadar Sama Ta K/Nassarawa

Labarai da suke fitowa daga fadar gwamnatin Jihar Kano ta bakin kwamishinan ma’aikatar ayyuka da gidaje Aminu Aliyu Wudil yace gadar sama ta kofar Nassarawa tana cikin hadari sakamakon budewa da tayi

Tawagar gwamnati da ‘yan kwangilar da suka gina gadar sunyi tattaki domin ganewa idanuwansu, tare da bada shawara yadda za’a kai ga samun mafita.

Don haka, ana kira da masu amfani da wannan gadar sama ta K/Nassarawa suyi hankali.

MU FARA TAFA MASA, SANNAN SAI MUYI MASA ADDU’A

Wannan mutumin da kuke gani sunansa Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina, shine mai kamfanin Jiragen sama na AZMAN AIRLINES, mutane irinsa alheri ne a cikin al’umma….

Dalibai Dari Biyu da ishirin da bakwai na jihar Kano ya biyawa kudaden biyan kudin karatu a jami’ar Bayero dake Kano….

Ance dukkan daliban da aka biyawa sai da aka tabbatar ya’yan talakawa ne sannan aka zabesu aka biyamusu kudaden….

Allah ya saka masa da alheri, ya karamana masu arziki irinsa a cikin al’ummarmu….

Neman Qahon Kare

A wata makaranta ne awaki 3 suka shigo domin yin kiwo, sai wasu ‘yan makarantar suka gansu, suka kamasu sai suka yanke shawara su yi wa awakin shaida.

Suka nemi fenti suka zanawa kowacce daya daga cikin awakin lamba a jikinta kamar haka; ta fari aka zana mata lamba (1) ta biyu lamba (2) sai ta uku lamba (4) bayan sun zanawa kowacce lambar ta sai suka sakesu, kowa ya tafi abinshi.

Awaki suka tafi cikin makarantar sukaci gaba da kiwonsu, bayan tsayin wani lokaci, sai mahukuntar makarantar suka shigo domin duba dalibai da sauransu, suna zagawa cikin makarantar sai sukayi karo da awakin.

Mahukuntan sukayi mamaki yadda awaki suka shigo makarantar, sai suka bada umarnin a kama awakin a fiddasu daga makarantar, nan take ma’aikata suka kamasu, amma abin mamaki shine kowacce akuya akwai lambarta a jikinta.

Ga mai lamba 1, ga mai lamba 2, ga mai lamba 4, amma babu mai lamba 3, shine akace to mai lamba 3 tana cikin makarantar lallai a nemota, akayi neman duniya ba’aga mai lamba 3 ba, haka akayi ta nema har tsayin dogon lokaci, harma takai kara fito da sauran ma’aikatan makarantar domin tsaurara bincike amma shiru ba’a sami mai lamba 3 ba, dalili kuwa saboda dama can babu ita.

Wannan Qalubale ne ga Al’ummah a harkar rayuwa, ilimi, kasuwanci, aikin yi da sauran abubuwa.

Ya zama wajibi mu tsaya akan abinda yazo hannunmu, mu daina hangen abinda bamudashi domin samun nutsuwa da zaman lafiya da cigaba a rayuwarmu.

Soyayyar Al’ummar mu Itace Kangaba

Wani labari da muka samu yanzu ya ruwaito cewa, akwai wani Bature mazaunin Najeriya tsayin shekaru 22 wanda yayi niyyar komawa garinsu a Kasar Turai.

Wannan Bature yana da maigadi ‘dan Najeriya wanda suka shafe tsayin wadannan shekaru tare, yana masa aikin gadi, sai Bature ya kira maigadi yace, nifa zan koma kasarmu don haka ka nuna inda kakeso zan gina maka gidan zama kai da iyalinka.

Abin mamaki sai maigadi yace shidai yafi bukatar Bature ya taimakawa Al’ummar garinsu ya samar musu da ruwan sha shine abinda yake ci musu tuwo a kwarya maimakon ya gina masa gida shi da iyalinsa kadai.

Nan take Bature ya amince, sukaje garin su maigadi aka nemi wajen da ya dace aka samar musu da yadda zasu sami ruwan sha, jin dadin da Bature yayi na ganin yadda maigadi ya damu da Al’ummar sa, sai yace da maigadi duk da samar musu da ruwan sha din da yayi ya kuma mallaka masa wannan gidan da shi Bature yake yake ciki.

Qalubale:

Mai gadi ya sami abubuwa guda biyu maimakon guda daya.

Mai gadi ya nuna soyayyar Al’ummar sa maimakon soyayyar kansa.

Bature ya nunawa mai gadi sadaukar da son rai zai iya samarwa mutum bukatarsa ta rayuwa.

Shin haka Al’ummar mu sukeyi a halin yanzu?

Yan Sanda Sun Kama Makamai A Ofisoshin PDP da APC

Yan sanda sunce sun kama makamai da suka hada da takubba, wukake, adduna da kuma kwayoyin da ake sha domin buguwa a ofisoshin jam’iyyun PDP da APC yayin da suka kai wani sumame a Karamar Hukumar Tudunwada a Jihar Kano.

Hukumar Yan sandan ta Jihar Kano ta bakin kakakinta DSP Haruna Abdullahi sunce, sun kai sumamen domin kokarin karkade miyagun ayyuka, haka kuma sun damke yan bangar siyasa guda hudu-hudu wadanda ake tuhuma da mallakar wadannan makamai a kowace sakatariya ta jam’iyoyin na PDP da APC.

A gefe guda Shugaban Jam’iyyar APC da Sakatare na riko a Jam’iyyar PDP sun karyata labarin cewa, ba mutanen su bane, kuma dama an saba yi musu wannan kazafi domin a kamasu ba tare da aikata laifin komaiba tun bayan kammala zabe bi-da-bi

ADAM A ZANGO Zaiyi AURE Karo Na shida 6

Fiteccen Jarimin Fina finan Hausa Na Masana’antar “Kanywood” zai Angonce Karo Na shida A ranar Juma’a Mai zuwa da Misalin karfe 2:30pm na Rana a fadar Mai Martaba Sarkin Gwandu dake jahar Kebbi
.
Adam A zango dai yayi aure 6 tun shekara ta 2006 kawo yanzu, Adam ya Auri Matarsa ta farko Amina a shekara ta 2006 kuma ta haifi Yaro mai suna Haidar wanda yanzu shekarasa 12, sai Amaryarsa ta biyu ita ce Aisha ‘yar SHIKA cikin Garin zariya jahar Kaduna wanda ta haifi ‘ya’ya uku 3 Maza
.
Akwai kuma Matarsa ta uku 3 Mai suna Maryam ‘yar jahar Nasarawa, haka zalika ya sake aure na 4 A Lugbe cikin Birnin Yola jahar Adamawa inda ya Auri Maryam AB,
.
Acikin shekara ta 2015 Adam A zango ya karayin Aure a sirrince inda ya auri wata mata mai suna Ummikulsum Mai shekaru 34 A garin Ngaoundere cikin kasar Kamaru kuma ta haifi Yarinya d’aya mai suna Murjanatu
.
Yanzu haka Adam A zango zai sake Angwancewa da Amaryarsa Safiyya Umar Chalawa wacce akafi sani da(Suffy) a ranar Juma’a mai zuwa
.
Bayanai dai sunce yanzu haka Adam A zango bashi da Mata ko d’aya sakamakon Sakinsu da yayi
.
Menene ra’ayinku Gamai da auren Adam A zango?

Design a site like this with WordPress.com
Get started