
Macijiya ce ta shiga shagon kafinta tana kutsawa sannu a hankali, cikin rashin lura sai tayi tuntube da zarto wanda hakan yaja sanadiyyar da wannan zarton ya dan karceta, cikin bacin rai Macijiya ta juyo ta kaiwa wannan zarto sara wanda hakan yayi sanadiyyar fitan jini a bakin Macijiya, kokarin neman daukar fansa yasa wannan Macijiya ta nannaɗe wannan zarton da nufin tayi mika don ta karairayashi sai dai kuma kash! hakan yayi sanadiyyar rasa rayuwarta ba tare da wannan zarto yaji koda kwarzane ba.
Jan hankali: so da yawa mukanyi saurin fushi da kokarin hanzarin daukar fansa hatta akan wanda ya saba mana cikin kuskure, kuma mu dage akan sai mun dau fansa wanda da yawa hakan kan sanya ƙaiƙayi ya koma kan mashekiya.
# Ba’a komai ake daukar fansa ba kamar yadda, saurin fishi kan sanya muguwar nadama.
Qalubale@gmail.com

Pretty! Thhis has been an incredibly wonderful article.
Many thanks for providing this information.
LikeLike