Daga Umar Faruq Muhammad:

Duk Mai hankali in ya kalli ‘Caption’ din da Premium Times sukayi amfani dashi akan batun Batan Dan Gwagwarmaya Dadiyata zai fahimci akwai boyayyar Manufa cikin rubutun nasu.
Ina kira ga Makusantan Gwamna Ganduje don Allah subawa Gwamna shawara yasa Alkalai su tuhumi Mawallafan Premium Times meyasa suka alakanta batan da sunan sa?
Dadiyata Dan Jihar Kaduna ne, kuma a Jihar Kadunan yake rayuwa, hakanan ba Gwamnatin Kano kawai yake suka ba a matsayin sa na Dan Jam’iyyar Hamayya ta PDP.
A Jihar Kano muna da Yan Jarida dasuka caccaki Gwamna Ganduje tun a lokacin dayake neman Kuri’u har zuwa lokacin da ake Shari’a a Tribunal, amma kuma babu wanda yagamu da wani abu na rashin jin dadi daga Gwamnan.
Don haka nake fatan Allah yasa Gwamna Yakarbi shawarar neman hakkinsa daga premium Times.
SSA Auwal Lawan Aranposu da Hon Abubakar Aminu Ibrahim a taimaka amikawa Gwamna wannan bukatar tawa.
Qalubale@gmail.com
